Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 19:10:41    
Rahoton gwamnatin kasar Sin yana tabbatar da fararen hula za su sami sakamakon cigaban kasar

cri

Bugu da kari kuma, bisa rahoton da Mr. Wen Jiabao ya gabatar wa wakilan jama'a, a cikin shekaru 5 da suka gabata, matsakaicin saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 10.6 cikin kashi dari, yawan matalauta yana ta raguwa a kowace shekara a kai a kai. An daina buga haraji kan manoma wadanda suke noman amfanin gona. Haka kuma, yawan kudaden shigi da fici da kasar Sin ta samu a shekarar 2007 ya kai matsayi na 3 a duk fadin duniya. Sannan kuma, kasar Sin ta samu nasarorin harba kumbon sararin sama mai daukar mutane da taurarin dan Adam na binciken duniyar wata. Kazalika kuma, kasar Sin ta cimma burin ba da ilmin tilas a kauyuka ba tare da karbar kudin karatu ba, kuma yawan karin mutanen da suka samu aikin yi a garuruwa da birane ya kai miliyan 51 a cikin shekaru 5 da suka gabata. Mr. Wen ya ce, dalilan da suka sanya kasar Sin ta samu wadannan manyan cigaban da suke jawo hankulan duk duniya su ne, "Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin 'yancin tunanin mutane da neman cigaba ta hanyar kimiyya da aiwatar da manufofin yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje da kuma aiwatar da manufofin sa ido kan tattalin arziki daga dukkan fannoni da kuma tsayawa tsayin daka kan matsayin mulkin kasa domin moriyar jama'a da aiwatar da harkokin gwamnati bisa doka."

A cikin wannan rahoton aiki, Mr. Wen Jiabao ya kuma mai da hankali sosai kan batutuwa iri iri da suke kasancewa a gaban gwamnatin kasar, kamar su saurin karuwar tattalin arziki da raguwar darajar kudin kasar, wato Renminbi yuan da hauhawar farashin kayayyaki da ilmi da samar da guraban aikin yi da kiwon lafiya da wurin kwana da karuwar kudin shiga da fararen hula suke samu da dai makamatansu.


1 2