Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 19:10:41    
Rahoton gwamnatin kasar Sin yana tabbatar da fararen hula za su sami sakamakon cigaban kasar

cri

A gun taron shekara-shekara na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka fara yi tun daga yau, wato ran 5 ga wata da safe, firayin ministan gwamnatin kasar Mr. Wen Jiabao ya wakilci gwamnatin tsakiya wadda za a kawo karshen wa'adinta na aiki ya gabatar da wannan rahoton aiki na gwamnati. A cikin wannan rahoto, an yi amfani da hakikanan abubuwa da kididdiga lokacin da ake bayyana ayyukan da gwamnatin ta yi a cikin shekaru 5 da suka gabata. A waje daya kuma, an dauki hakikanan matakai da shawara kan yadda za a yi ayyukan shekarar da muke ciki. Wakilai mahalartar wannan taro suna ganin cewa, wannan rahoto yana mai da hankali kan yadda za a daidaita sabbin matsaloli da kawar da wahalhalu, sannan kuma yana mai da hankali sosai kan moriyar fararen hula kwarai.

An nada Wen Jiabao firayin ministan gwamnatin kasar Sin ne a watan Maris na shekarar 2003. Bisa tsarin mulkin kasar Sin, wa'adin aiki na firayin ministan gwamnati ya kai tsawon shekaru 5. Lokacin da yake waiwayen ayyukan da gwamnatinsa ta yi a cikin shekaru 5 da suka gabata, Wen Jiabao ya ce, wadannan shekaru 5 ba na yau da kullum ba ne. A cikin farkon rahotonsa, bai ambata cigaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki ba, amma ya ambaci yadda aka yi fama da ciwon SARS da ya auku a farkon rabin shekarar 2003 da bala'in dusar kankara da ya auku a watan Janairu na shekarar da muke ciki. Wakilan jama'a da yawa sun ce, wannan ya bayyana cewa, gwamnatin yanzu ta fi mai da hankali kan moriyar fararen hula. Mr. Wang Shoubing, wani wakilin jama'a da ya zo daga lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin ya ce, "Bayan da gwamnatin yanzu ta fara aiki ba da dadewa ba a shekarar 2003, ta samu matsalar ciwon SARS a duk fadin kasar da ba a taba gani ba a da. Musamman wannan bala'in dusar kankara da ya auku a shekarar da muke ciki, bala'i daga indallahi ne mai tsanani sosai. Gwamnatinmu ta daidaita su kamar yadda ake fata, wannan ya almanta cewa, gwamnatin yanzu tana da kwarewar daidaita matsalolin da suke faruwa ba zato ba tsammani, kuma tana mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a sosai."

1 2