Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 18:48:18    
Za a kira taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ba da jimawa ba

cri

Kullum a kan kira cikakken zama na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ko wace shekara, amma shekarar da muke ciki shekara ce da aka samu wakilai na sabon zama, shi ya sa taron ya jawo hankulan bangarori daban daban sosai. Lokacin da yake ambaci ajandar taron, Mr. Jiang ya bayyana cewa, "Akwai ajandu 16 a gun taron, ciki har da tattaunawa kan rahoton aiki na gwamnatin kasar Sin, da tattaunawa kan shirin gyare-gyaren hukumomin majalisar gudanarwa ta kasar, da zaben shugaban kasar, da kuma nada firayim ministan kasar."

Bugu da kari kuma taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da za a yi a shekarar nan ya jawo hankulan manema labarai na gida da na waje kwarai da gaske, yawan manema labarai da suka yi rajista ya zarce na shekarar bara sosai. Bisa labarin da muka samu daga cibiyar manema labarai ta taron, an ce, ban da kafofin watsa labarai na kasar Sin, manema labarai fiye da dubu daya na kafofin watsa labarai 225 da suka zo daga kasashe fiye da 40 sun yi rajista don shiga taron. Wakilin farko na gidan rediyo na kasar Amurka wato NPR da ke kasar Sin Anthony Kuhn ya gaya mana cewa, "A hakika dai, an amince da manema labarai na kasashen waje da mu shiga tarurukan kungiyoyi daban daban na majalisar a 'yan shekarun nan da suka gabata, wannan ya samar da wata kyakkyawar dama gare mu wajen tuntubar wakilai daban daban."(Kande Gao)


1 2