Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 18:48:18    
Za a kira taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ba da jimawa ba

cri

A ran 5 ga wata, za a kira taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a birnin Beijing, wadda ta kasance hukumar koli ta kasar Sin. Kakakin taron Jiang Enzhu ya yi bayani a ran 4 ga wata a birnin Beijing, cewa yanzu an riga an kammala dukkan ayyukan share fage ga taron. To, yanzu ga cikakken bayani.

A ran 3 ga wata da safe, wakilai masu halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar Sin na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta sun iso birnin Beijing ta jirgin kasa. Sabo da haka, dukkan wakilan jama'a na sabon zama na majalisar kusan 3000 sun iso birnin. Kakakin taron Jiang Enzhu ya yi bayani a gun taron manema labarai da aka shirya a ran 4 ga wata a brinin Beijing cewa, "Za a kira taron gobe wato ran 5 ga wata da safe, haka kuma za a rufe shi a ran 18 ga wata da safe, sabo da haka taron zai shafe kwanaki 13 da rabi. Ya zuwa yanzu, an riga an share fage sosai ga taron."

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin hukuma ce ta koli ta kasar inda jama'ar Sin ke iya gudanar da ikon mulkin kasar. Majalisar tana kunshe da wakilan jama'a na duk fadin kasar Sin, wadanda suke iya gudanar da ikon mulkin kasar gaba daya. Haka kuma a kan samu wakilan jama'a ta yin zabe na demokiradiyya, wadanda suka zo daga yankuna da sana'o'i da kabilu daban daban na kasar Sin, kuma wa'adin aikinsu shi ne shekaru biyar. Gabatar da shawarwari bisa doka wani muhimmin aiki da kuma muhimmin hakki ne gare su.

Jiang Enzhu ya bayyana cewa, "A cikin shekaru biyar da suka gabata, wakilai sun gabatar da shirye-shirye fiye da 3700 da kuma shawarwari kusan dubu 30, an kafa dokoki bisa wasu shirye-shiryen doka daga cikinsu, da kuma gyara dokoki bisa shawarwarin. Ban da wannan kuma wakilan jama'a fiye da 660 sun halarci taron zaunannen kwamitin na majalisar wakilan jama'ar kasar, wakilai fiye da 1700 sun sa hannu a cikin ayyukan bincike bisa doka da kuma gudanar da bincike don kafa dokoki. Ta wadannan harkoki, an kyautata karewar wakilai wajen gudanar da aiki, kuma an yada amfaninsu sosai wajen sa hannu a cikin ayyukan gudanar da harkokin kasa."

1 2