Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-27 16:56:12    
Ana himmantuwa wajen share fage ga gudanar da gasar sukuwar dawaki ta taron wasannin Olympic a yankin Hongkong

cri

Club din sukuwar dawaki na Hong Kong dake da dadadden tarihi ya da alhakin dake bisa wuyansa na sa ido kan aikin gina filin gasar sukuwar dawaki a wannan gami. Sufeto-janar na club din Mr. Kim K. W. Mak ya furta cewa: " Za a gudanar da gasa irin ta jarrabawa nan gaba kadan. Ana gina filin wasan ne daidai bisa tsarin da aka tsara a da, inda kuma akwai gidajen dawaki sama da 200 da kuma iyakwandishan. Ban da wannan kuma, yanzu ana kayatar da dakunan bada magani na dawaki. Dadin dadawa, an rigaya an kammala ayyukan gina filayen horaswa fiye da 10. Saboda da haka ne, muke cike da imanin cewa za a gudanar da gasa irin ta jarrabawa cikin nasara".

Mr. Lam Woon Kwong, babban jami'in zartaswa na kamfanin kula da harkokin wasan sukuwar dawaki na taron wasannin Olympic ya fadi, cewa gasar sukuwar dawaki dai, wata irin gasa ce mafi sarkakiya a cikin dukkan manyan ayyukan wasa 28 na taron wasannin Olympic. A cewarsa, gasar sukuwar dawaki ba ma kawai na shafar 'yan wasa ba, har ma na shafar dawaki. Lallai abun zai zama mai sarkakiya idan aikin shirye-shiryen harkokin gasar sukuwar dawaki ya shafi dabbobi. Tun bayan da aka kafa wannan kamfani, mutanen dake cikinsa suna aiki ba dare ba rana, wassu jami'an kamfanin ma suna kai da kawowa tsakanin Beijing da Hong Kong domin ayyukan da abin ya shafa. Wadanda suke tuntubar sun hada da kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa , da hadaddiyar kungiyar kula da harkokin wasan sukuwar dawaki ta duniya, da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing, da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong da kuma kwamitin wasannin Olympic na Hong Kong da dai sauran hukumomin da abin ya shafa.


1 2 3