Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-19 19:19:25    
Sin tana kokarin tsugunar da jama'ar da bala'i ya shafa yadda ya kamata

cri

A kwanakin baya jare, ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya ya afkawa yankuna da dama da ke kudu maso tsakiyar kasar Sin, wanda ya zuwa yanzu ya rutsa da jama'a sama da miliyan 100, tare kuma da rushe gidaje fiye da dubu 300. Tun bayan aukuwar bala'in a karshen watan Yuni da ya wuce, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da kuma hukumomin wurare daban daban sun fara aiki da tsarin yaki da bala'in cikin lokaci, suna kokarin ba da jagoranci kan ayyukan yaki da ambaliyar ruwa da kuma ba da agaji, kuma yanzu an tsugunar da daukacin jama'ar da bala'in ya shafa yadda ya kamata.

Yankunan da kogin Huaihe ya ratsa da ke tsakiyar kasar Sin sun kasance yankunan da aka fi fama da ambaliyar ruwa a halin yanzu. Kogin Huaihe ya ratsa lardunan Henan da Anhui da Jiangsu na kasar Sin wadanda ke da dimbin jama'a, kuma ambaliyar ruwan ta kawo manyan hasarori ga jama'ar wurin, amma gwamnatin kasar Sin tana kokarin yaki da ambaliyar ruwa da kuma tsugunar da jama'ar da bala'in ya shafa a wurin.

"gwamnati ta kawo mana shinkafa da taliya da ruwan sha da kayan lambu da albasa da Tumatir da dai sauransu duka, ta tsugunar da mu yadda ya kamata."Wannan shi ne abin da Zhang Zhifu, wani manomi da ke yankin Mengwa na karkarta da ambaliyar ruwa da ke garin Fuyang na lardin Anhui na kasar Sin, ya fada wa wakilinmu, yayin da yake bayyana yadda aka tsugunar da su. Zhang Zhifu ya yi manyan hasarori sakamakon ambaliyar ruwa, amma yana imani da cewa, gwamnati za ta taimake su wajen haye wahalar.


1 2 3