Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 15:19:16    
Hanyar ruwa ta Lingqu a birnin Guilin

cri

Hanyar ruwa ta Lingqu ta hada da wata madatsar ruwa mai suna Huatou da hanyar ruwa ta kudu da ta arewa da kuma sauran wurare masu ni'ima. Siffar madatsar ruwa mai suna Huatou ta yi kama da wani irin kayan aikin gona wai shi ploughshare. Madatsar ruwan nan na matsayin rarraba ruwan da yawansa ya kai misalin kashi 70 cikin kashi dari zuwa kogin Xiangjiang ta hanyar ruwa ta arewa, sa'an nan kuma, ta rarraba ruwan da yawansa ya kai misalin kashi 30 cikin kashi dari zuwa kogin Lijiang ta hanyar ruwa ta kudu.

An dasa itacen peach da willow a kan gabobin hanyar ruwa ta Lingqu. A lokacin bazara na ko wace shekara, ana iya ganin furannin peach blossom masu ruwan hoda da kwarran ganyayen itacen willow a cikin ruwa mai tsabta. Itacen peach da willow da kuma inuwarsu da suka bullo a cikin ruwan sun zama wani zane mai kyan gani kuma mai ban sha'awa.(Tasallah)


1 2