Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 15:19:16    
Hanyar ruwa ta Lingqu a birnin Guilin

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan wata hanyar ruwa da ke birnin Guilin na jihar kabilar Zhang ta Guangxi mai tafiyar da harkokinta da kanta. Daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka 'Kyakkyawan birni na Chongqing', wanda shirinmu ne na musamman na 'birnin Chong Qing a yau', mun shirya shi ne domin murnar cikon shekaru 10 da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta fara shugabantar Chongqing kai tsaye.

An shimfida hanyar ruwa ta Lingqu mai tsawon kilomita 34 a shekarar 219 zuwa ta 214 kafin haihuwar Annabi Isa A.S.. Ita ce aikin yin amfani da ruwa mafi inganci da aka adana ta yadda ya kamata a duk duniya a yanzu. An yi zane-zane a kanta ta hanyar kimiyya, an kuma shimfida ta kamar yadda ya kamata. Hanyar ruwan nan ta hada tsare-tsaren ruwa na kogunan Yangtze da Zhujiang, sa'an nan kuma, ta taba taka muhimmiyar rawa a matsayin cibiyar sadarwa a tsakanin tsakiyar kasar Sin da kuma yankin Lingnan tun daga daular zamanin Qin wato tsakanin shekarar 221 zuwa ta 206 kafin haihuwar Annabi Isa A.S.. A shekarun baya da suka wuce, saboda hukumar gundumar Xing'an ta jihar kabilar Zhang ta Guangxi mai tafiyar da harkokinta da kanta ta zuba kudin da yawansa ya kai misalin kudin Sin yuan miliyan 30 domin kiyaye hanyar ruwa ta Lingqu ta fuskar muhalli da kuma raya aikin yawon shakatawa a nan, shi ya sa wannan hanyar ruwa ta zama sabon wurin yawon shakatawa da ke jawo hankulan mutane a birnin Guilin.


1 2