Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-09 21:47:44    
Kasar Sin mai bunkasuwa da Birnin Beijing mai ci gaba

cri

"A shekarar 1976, na kai ziyara karo na farko a birnin Beijing, a wancan lokaci birnin Beijing ba kamar na yanzu ba, wato ba shi da gidaje layi-layi, kuma ba shi da hanyoyi masu fadi, hanyar da aka shimfida daga filin jirgin sama zuwa tsakiyar birnin ba kamar ta yanzu ba, wato yanzu hanyoyin motoci sun ratsa ta ko'ina, amma a da babu motoci da yawa, muhimmin kayan da aka yi amfani da shi domin tafiya shi ne basukur. Ire-iren tufaffin da Sinawa suka sa a wannan lokaci ma ba su da yawa, a takaice dai ba a iya kwatanta birnin Beijing na da da na yanzu ba ko kusa."

Mr. Hassan yana da ilmi mai zurfi, bisa matsayinsa na wani abokin aikinmu mai fasahohi da yawa wajen watsa labaru, shi ma yana kulawa da shirye-shiryen gidan Rediyon kasar Sin sosai, kuma ya yaba sosai ga amfanin gidan Rediyonmu bisa taimakon da ya bayar wajen watsa labaru ga kasashen waje, ya ce,

"Rediyon kasar Sin ya gabatar da kasar Sin ga duniya ta harsuna kasashe daban-daban, ta yadda masu sauraron kasashen waje za su fahimci manyan nasarorin da kasar Sin ta samu daga fannoni daban-daban."(Umaru)


1  2  3