"Wannan taron koli na Beijing wani babban al'amari ne ko ga kasar Sin ko kuma ga Afirka. Sabo da haka, domin tabbatar da samun nasarar wannan taro, kasar Sin ta nuna goyon bayansa daga duk fannoni, cikin har da gabatar da sharuda masu sauki ga manema labaru na kasashe daban-daban don su ba da labaru ga wannan taro, wadannan matakan da aka dauka sun ba da babban taimako ga manema labaru na kasashe daban-daban da su ba da labaru game da wannan taron koli daga duk fannoni kuma a daidai lokaci kuma ta tsararriyar hanya."
Mr. Hassan ya bayyana cewa, nasarar da aka samu wajen wannan taron koli za ta jawo babban tasiri ga Afirka, har ma ga duk duniya baki daya. Ya bayyana cewa, zai dukufa kan aikin kara fadakar da jama'ar Masar ga taron dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afirka, ta yadda za su kara fahimtar kasar Sin sosai.
A lokacin da Mr. Hassan yake amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa, ya tuna da tarihin ziyarar da ya taba yi wa kasar Sin har sau 2, musamman ma ya tabo magana cewa, sauye-sauyen da aka samu a nan birnin Beijing sun ba shi zurfaffiyar alama a zuciyarsa. Ya ce,
1 2 3
|