Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 19:39:24    
Sabuwar huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare hulda ce mai muhimmanci

cri

Don ingiza bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka da ke tsakanin Sin da Afirka bisa muhimman tsare-tsare, kasashen Sin da Afirka sun tsai da kudurin kara hadin gwiwa a fannoni daban daban, za su daga matsayin hadin gwiwarsu.

A cikin sabon halin da ake ciki, kasashen Sin da Afirka suna da makasudin bunkasuwa iri daya, suna kara samun moriya bai daya, suna kara bukatar juna. Kulla sabuwar dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare bukata ce wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu, kuma bukata ce ta tilas wajen sa kaimi kan zaman lafiya da bunkasuwar duniya, sa'an nan kuma, ta zama kyakkyawan misali wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Kasashen Sin da Afirka suna kara bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu, wannan yana amfana wa ci gabansu, har ma yana amfana wa sa kaimi kan hada kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, ya amfana wajen gaggauta samar da sabon odar siyasa da tattalin arziki na duniya mai adalci yadda ya kamata, ya amfana wajen sa kaimi kan bunkasuwar duniya mai jituwa da wadatuwa. Sin da Afirka suna hada kansu a fili kuma a bayyane yadda ya kamata, irin wannan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ba zai kawo illa ga hadin gwiwar da ke tskaninsu da sauran kasashe ba, kuma ba zai kawo illa ga moriyar sauran kasashe ba. A maimakon haka, kasashen Sin da Afirka za su kawo wa kasashen duniya dama mai kyau a sakamakon kara hada kansu da samun ci gaba tare.

Sabuwar dangantakar abokantaka da ke tsakanin Sin da Afirka bisa muhimman tsare-tsare za ta ba da sabuwar gudummawa wajen tabbatar da ci gaban Sin da Afirka da jin dadin jama'ar su da kuma sa kaimi kan raya duniya mai zaman lafiya da wadatuwa da jituwa cikin dogon lokaci.(Tasallah)


1  2  3