Muhimmin sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka shi ne a cikin 'sanarwar taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka' da suka bayar a ran 5 ga wata, a hukunce ne shugabannin Sin da Afirka suka sanar da kafa da kuma raya sabuwar dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa muhimman tsare-tsare, za su yi zaman daidai wa daida da amincewa da juna a fannin siyasa, da yin hadin gwiwa don cin nasara tare a fannin tattalin arziki, da kuma yin mu'amala da koyi da juna a fannin al'adu. Wannan ya alamta cewa, Sin da Afirka sun rika zurfafa dangantakarsu, har ma ta shiga sabon mataki, tana da muhimmiyar ma'ana ta halin yanzu da kuma ma'anar tarihi mai zurfi.
Kasashen Sin da Afirka sun kafa dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare a tsakaninsu bisa tushe na kyakkyawar zumunci da hadin kai da hadin gwiwa da ke tsakaninsu.
1 2 3
|