Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 22:01:25    
An bude taron manyan kusoshi na biyar na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika

cri

A cikin nasa jawabin, Malam Haile-Kiros ya bayyana cewa, tun bayan da aka kira taron ministoci na karo na biyu na dandalin tattaunawar, an yi ta samun ci gaba wajen hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika don moriyar juna. Ya kara da cewa, "shugabannin Sin da na kasashen Afrika za su iya shirya babban taron koli kamar haka a birnin Beijing, wannan ya nuna muhimmancin aminci da ke tsakanin Sin da kasashen Afrika. Ba ma kawai taron koli na Beijing ya nuna muhimmanci da shugabannin Sin da na kasashen Afrika ke dora ga dangantakar da ke tsakanin bangarorin nan biyu ba, har ma ya nuna cewa, an kulla dangantakar aminci a tsakanin Sin da kasashen Afrika ne bisa tushe mai karfi, kuma bisa halin da ake ciki don fuskantar karni na 21."

Ka zalika a wannan rana, shugaban kasar Sin Hu Jintao da firayim minista Wen Jiabao ko wanensu ya gana da shugabannin kasashen Afrika da yawa a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Guiena Bissau da ta Gabon da Liberiya da Komoro da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika ko wanensu ya yi tattaunawa tare da shugabannin kasar Sin a kan yalwata dangantaka da ke tsakanin bangarori biyu da huldar tsakanin Sin da Afrika da kuma taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika. (Halilu)


1  2