Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 22:01:25    
An bude taron manyan kusoshi na biyar na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika

cri

Ran 1 ga wata, an bude taron manyan kusoshi na karo na biyar na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika, wanda za a shafe kwanaki biyu ana yinsa a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Wakilan kasashen Afrika 48 na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika da jakadun kasashen Afrika a kasar Sin misalin 200 sun halarci wannan taro. Taron nan wani taro ne mai muhimmanci ga dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika. A gun taron, za a dudduba takardu da abin ya shafa, don share fage a karo na karshe ga taron koli da taron ministoci na karo na uku na dandalin tattaunawar nan.

Madam Xu Jinghu, babbar sakatariyar kwamitin kasar Sin mai kula da harkokin taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika da Malam Haile-Kiros, manzon musamman na kasar Habasha wadda ke shugabancin taron dandalin tattaunawar nan tare da sauran kasashe, kuma jakadan kasar Habasha a kasar Sin sun hada guiwa sun shugabanci taron manyan kusoshi na karo na biyar na dandalin tattaunawar. A gun taron, da farko, Madam Xu Jinghu ta yi kyakkyawar maraba da wakilan taron da jakadun kasashen Afrika. Ta ce, "a madadin sakatariyar kwamitin kasar Sin mai kula da harkokin taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika, nake yin kyakkyawar maraba da duk wakilan taron da jakadun kasashen Afrika daban daban. "

Malam Zhai Juan, babban sakataren kwamitin Sin mai kula da harkokin shirya taron koli na Beijing kuma mataimakin ministan harkokin waje na kasar da Malam Haile-Kiros, manzon musamman na kasar Habasha ko wanensu ya yi jawabin fatan alheri a gun bikin bude taron. A cikin jawabinsa, Malam Zhai Juan ya nuna babban yabo ga kyakkyawan sakamako da aka samu tun bayan da aka fara yin taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika har a cikin shekaru 6 da suka wuce. Ya ce, "bisa kokarin da bangarorin Sin da Afrika suka yi a cikin shakaru 6 da suka wuce, sun kara amincewa da juna a fannin siyasa, sun yalwata huldar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu cikin sauri, sun inganta hadin guiwarsu yadda ya kamata a fannoni daban daban, sun kara dankon aminci da ke tsakaninsu a karkashin inuwar taron dandalin tattauwar zuwa wani sabon mataki. Taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika ya riga ya zama wani tsari mai yakini na yin tattaunawa a tsakanin bangarori biyu da wani dandali mai muhimmanci ga inganta hadin guiwarsu yadda ya kamata. Ba ma kawai taron dandalin tattaunawar nan ya kara dankon amincin gargajiya a tsakanin Sin da Afrika ba, har ma ya samar da sabuwar dama ga inganta hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika don neman samun bunkasuwa, bisa sabon halin da ake ciki. "

1  2