Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-31 19:10:16    
Kasar Kenya tana maraba da masu yawon shakatawa na kasar Sin da hannu biyu-biyu

cri

A cikin shekarun nan da suka wuce, kasar Kenya tana daukar matakai iri daban daban don raya aikin yawon shakatawa da ya zama gishiki ne na tattalin arzikin kasar. wani muhimmin matakin da take dauka shi ne kara jawo masu yawon shakatawa na kasar Sin da su kai wa kasar Kenya ziyara.

A matsayin wata kasa mai yawan albarkatun yawon shakatawa, aikin yawon shakatawa yana taka muhimmiyar rawa a cikin tattalin arzikin kasar Kenya. Yawancin masu yawo shakatawa da suka ziyarci kasar Kenya a da mutane ne da suka zo daga kasashen Turai da Amurka, amma a cikin 'yan shekarun nan da suka shige, saboda kasashen Sin da Kenya sun rika karfafa dangantakar da ke tsakaninsu, shi ya sa mutanen Sin suke kara zuwa kasar Kenya don yin yawon shakatawa, wannan ya sanya rukunoni daban daban na kasar Kenya su fahimci babban karfin da kasuwar kasar Sin ba ta taba nunawa a da ba, shi ya sa dukan shugaban kasar da kuma jami'an yawon shakatawa na kasar Kenya sun gabatar da albarkatun yawon shakatawa ga kasar Sin a wurare daban daban. A lokacin da yake ziyarar kasar Sin a watan Agusta na shekarar bara, shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki ya halarci bikin kaddamar da tashar internet da hukumar yawon shakatawa ta kasar Kenya ta shirya cikin Sinanci, wadda tashar internet ce ta farko da kasar Kenya ta shirya cikin harshen waje. Kuma sau da yawa ne tsohon ministan yawon shakatawa na kasar kuma ministan harkokin waje na kasar na yanzu Raphael Tuju ya bayyana cewa, kasar Sin mai yawan mutane biliyan 1 da miliyan dari 3 wata kasuwa ce mai samar da masu yawon shakatawa, wadda take nuna babban karfin da ba ta taba yin amfani da shi ba, yana sa ran alheri domin ganin mutanen kasar Sin za su kara zuwa kasar Kenya don yin yawon shakatawa. Lokacin da yake zantawa da wakilimmu, sakataren kula da dangantakar da ke tsakanin ofishin shugaban kasar da al'ummar kasar kuma kakakin gwamnatin kasar Alfred N. Mutua ya yi wa masu yawon shakatawa na kasar Sin gayyata da hannu biyu-biyu. Ya ce,(murya ta 2, Mutua)

'Muna maraba da mutanen Sin da su yi yawon shakatawa a kasarmu, wadda kasa ce da ke nuna halin musamman sosai. Jama'ar Kenya suna maraba da jama'ar Sin da hannu biyu-biyu a ko wane lokaci, za mu sanya bakimmu na kasar Sin su mayar da kasar Kenya tamkar garinsu na biyu.'

Bisa kididdigar da hukumar yawon shakatawa ta kasar Kenya ta bayar, an ce, yawan mutanen kasar Sin da suka je kasar Kenya don yin yawon shakatawa a shekarun nan da suka wuce ya karu cikin sauri, wannan adadi ya karu daga misalin 2,600 na shekarar 2002 zuwa misalin 9,000 na shekarar 2004, adadin ya karu da sau biyu a cikin shekaru 3. Bayan da kasar Sin ta mayar da kasar Kenya a matsayin wurin shakatawa ga mutanen Sin a shekarar 2004, mutanen Sin da yawansu ya kai 11,000 sun kai wa kasar Kenya ziyara a shekarar 2005. Karuwar yawan masu yawon shakatawa na kasar Sin ta sa kaimi kan farfado da aikin yawon shakatawa na kasar Kenya har da bunkasuwar tattalin arzikinta.

1  2  3