Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-05 16:51:30    
Rahoton da Wen Jiabao ya yi kan aikin gwamnati dangane da batun rayuwar jama'a

cri

A wajen takaita ayyukan da aka yi a shekarar da ta shige, firayim minista Wen Jiabao ya takaita cewa, halin da aka ciki a shekarar 2005 ya bayyana cewa, tattalin arziki ya sami karuwa da saurin gaske, sakamakon da aka samu na da kyau sosai, kuma farashin kayayyaki ya zama a gindinsa, daga adadin da rahoton ya fayyace, ana iya ganin cewa, kudin shiga da mazaunan birane da kauyuka suka samu sai kara karuwa suke yi a bayyane, ya kuma tabbatar da kokarin da gwamnati ta yi a shekarar da ta shige wajen daidaita muhimman batutuwan da suka faru a lokacin da aka aiwatar da harkokin tattalin arziki da sa kaimi cikin himma da kwazo ga daidaita tsarin tattalin arziki da hanyoyin kara karuwarsa, a sa'I daya kuma ya bayyana cewa, ana kara samun wahaloli wajen kara karuwar girbin hatsi da kara wa manoma kudin shiga, jama'a sun kuma gamu da wuya wajen ganin  likitoci da kuma kudin makaranta na da tsada har ma halin da ake ciki wajen yin aiki cikin lafiya ya yi tsanani sosai, duk wadannan bai boye su ko kadan ba.

Shirin karuwar tattalin arziki da rahoton ya tsai da a shekarar da muke ciki ya kai kashi 8 cikin dari, a sa'I daya kuma ya gabatar da cewa, ya kamata a rage yawan makamashin da za a yi amfani da shi don kara GDP da kashi 4 cikin dari . Rahoton ya kasa muhimman ayyuka na shekarar da muke ciki sassa guda 8 , ciki har da sa kaimi ga raya sabbin kauyuka da kara karfi ga daidaita tsarin masana'antu da yin tsimin albarkatan halittu da kiyaye muhalli da kuma ci gaba da sa kaimi ga yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa da mai da hankali ga daidaita batutuwa dangane da moriyar jama'a ta hakika, wannan ya bayyana halin musamman da ke da amfani ga manoma da mai da muhimmanci ga ba da ilmi da kawar wahaloli , wannan kuma ya dace da kokarin da gwamnati ta yi wajen aiwatar da harkokin mulki don neman adalci a zamantakewar al'umma da samun bunkasuwa cikin jituwa da dai sauransu , duk wadannan halayen musamman an yi bayyanuwarsu ne a cikin tunanin raya kasar Sin a cikin shekaru biyar masu zuwa.


1  2  3