Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-15 17:23:08    
Abbas yana shirin rushe kungiyoyin dakaru daban daban na Palasdinu

cri

Aikin rushe kungiyoyin dakaru masu tsatsauran ra'ayi nauyin ne da ke bisa wuyan bangaren Palasdinu da aka tanada a cikin shirin "Taswirar hanyar shimfida zaman lafiya" a Gabas ta Tsakiya. Bayan da Isra'ila ta janye jikinta daga zirin Gaza, ta gaggauta wajen kafa katangar wariya da habaka matsugunan Yahudawa da ke yammacin gabar kogin Jordan. A wannan halin da ake ciki yanzu wato kafin Isra'ila ta sami karin moriya, aikin sake gudanar da shirin "Taswirar hanyar shimfida zaman lafiya" a Gabas ta Tsakiya da yin shawarwari a kan kafa kasar Palasdinu da warware sauran matsalolin a tsakaninsu ya dace da babbar moriya ta Palasdinu. Amma Isra'ila tana tsayawa tsayin daka cewa, Palasdinu ta rushe kungiyoyin dakaru masu tsatsauran ra'ayi da farko, sa'an nan za ta sake yin shawarwari da Palasdinu. A sa'i daya kuma, a matsayin babban mai samun sulhuntawa a tsakaninsu, kasar Amurka ta kara yi wa bangaren Palasdinu matsi. A ran 14 ga wata a gun taron shugabanni na MDD da aka shirya, shugaban kasar Amurka Malam Bush ya bayyana a fili cewa, Isra'ila ta janye jikinta daga zirin Gaza shi ne mataki na farko da aka dauka, a halin yanzu dai, ya kamata dukkan Palasdinawa su hada kansu, su kafa wata gwamnati wadda ta iya samun sulhuntawa da Isra'ila. Sabo da haka ne, ya zama tilas ga Malam Abbas ya rushe kungiyoyin.

Amma bayan da aka bayar da wannan shiri, sai nan da nan kungiyoyin dakaru ciki har da kungiyar Hamas sun nuna kiyewa gare shi. Mahmoud Zahar, shugaban kungiyar Hamas a zirin Gaza ya yi gargadi cewa, idan sojojin kiyaye zaman lafiya na Palasdinu za su dauki niyyar yin gaba da kungiyar Hamas, to, za su fuskanci kiyewa daga dukkan Palasdinawa.

Game da haka, a ran 14 ga wata, ministan watsa labaru na Palasdinu Nabil Shaath ya sake nanata cewa, bayan da hukumar ikon al'umma ta Palasdinu ta daddale yarjejeniya da kungiyoyin daban daban, sai za ta iya kwace damararsu. Hukumar ba ta son tada yakin basasa domin haka.(Danladi)


1  2  3