Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-15 17:23:08    
Abbas yana shirin rushe kungiyoyin dakaru daban daban na Palasdinu

cri

Bisa labarin da muka samu, an ce, ban da kungiyar Hamas da dai sauran kungiyoyin dakaru masu zaman kansu, a halin yanzu dai ya kasance da kungiyoyin dakaru gomai a karkashin jagorancin kungiyar Fatah. Ko da yake hukumar ikon al'umma ta Palasdinu ta taba bayar da wani umurni cewa, kada a yi amfani da haramtattun makamai a wuraren jama'a, amma ba a kula da wannan ba ko kadan har zuwa yanzu. Dakarun su kan kai farmaki ga hukumomin gwamnati da tsare mutanen kasashen waje domin garkuwa da su, haka kuma su kan kai farmaki ga juna, to, wadannan danyen aiki ya hana jama'a samun zaman lafiya, kuma ya dakushe kwarjini na hukumar ikon al'umma ta Palasdinu sosai. A wani fage daban kuma, kungiyoyin dakaru daban daban suna yin abin da suke so, sun ki yarda da yin shawarwari cikin lumana da Isra'ila, sabo da haka ne, Palasdinawa ba su iya kafa wani dinkin kawance a gun shawarwarin ba, wannan ya bata moriyar duk Palasdinawa sosai. Bayan da Isra'ila ta janye jikinta daga zirin Gaza, wannan hali ya kara tsananta.


1  2  3