Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-05-15 17:14:13    
IMF ya nemi kasashe masu arziki da su dauki matakan daidaita batun gibin kasafin kudi cikin gaggawa

cri
A ran 14 ga wata, asusun ba da lamuni na kasa da kasa, wato IMF ya nemi kasashe masu arziki da su dauki matakkan daidaita batun gibin kasafin kudi cikin gaggawa. A waje daya, ya yi gargadi cewa, idan ba a iya daidaita wannan batu kamar yadda ya kamata ba, za a iya samun koma bayan tattalin arzikin kasashe masu arziki.

A cikin wani rahoton kasafin kudi na jama'a na kasashe daban daban da wannan asusun IMF ya bayar, an yi hasashen cewa, yawan gibin kasafin kudi da ke wuyan kasashe masu arziki zai kai kashi 110 cikin kashi dari bisa na jimillar GDP nasu a shekarar 2015 daga kashi 73 cikin dari a shekarar 2007.

Wannan rahoto ya ce, rikicin basusukan da kasar Girka ta ci ya bayyana cewa, ba a iya kyale tsananin rikicin basusuka da ake fuskanta ba. Idan kasashe masu arziki ba za su iya daukar matakai masu amfani a yadda za su iya rage yawan gibin kasafin kudi ba, to, saurin karuwar tattalin arzikinsu ya ragu da kashi 0.5 cikin dari. (Sanusi Chen)