Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 20:01:54    
Shugaban Kenya ya gana da Wang Zhaoguo

cri

A ran 10 ga wata a birnin Nairobi, shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki ya gana da memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma mataimakin shugaban zaunanen kwaimitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wang Zhaoguo. Inda Wang Zhaoguo ya ce, a shekarar 2006, kasashen biyu sun kafa huldar abokantaka ta kawo moriyar juna mai dorewa a tsakaninsu, wato ke nan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya ta shiga sabon zamani na bunkasuwa. Kasashen biyu sun yi ta zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin siyasa da tattalin arziki da ciniki da zaman al'umma da al'adu, kuma sun samu sakamako mai kyau. Kasar Sin tana son tinkarar kalubalen da rikicin hada-hadar kudi na duniya ya kawo tare da kasar Kenya don ingiza hadin gwiwar sada zumunci na cin moriyar juna a dukkan fannoni.

Mwai Kibaki ya furta cewa, kasar Kenya ta mai da kasar Sin matsayin kawarta ta ainihi, ya kuma nuna yabo ga kyakkyawan sakamakon da Sin ta samu wajen raya kasa, haka kuma ya nuna godiya ga tallafin da kasar Sin ta samar mata. Kasar Kenya tana son kara hada kai da kasar Sin wajen kara yin hadin gwiwa don kawo moriya ga kasashen biyu da kuma jama'arsu.(Lami)