Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 16:56:00    
Kasar Koriya ta arewa ta bukaci Koriyar ta kudu da ta nemi gafara game da musanyar wuta da aka yi a yammacin tekun kasar

cri
A ranar 10 ga wata, bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Yonhap na kasar Koriya ta kudu ya bayar, an ce, hedkwatar kwamandojin kasar Koriya ta arewa ta bukaci Koriya ta kudu da ta nemi gafara game da aikin musanyar wuta da aka yi a tekun Huanghai.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a wannan rana, hedkwatar kwamandojin sojojin kasar Koriya ta arewa ta ba da sanarwa, inda aka bayyana cewa sojojin ruwan Koriya ta kudu sun yi tsokana ga kasar Koriya ta arewa a tekun kasar. Bayan da jiragen ruwa na sojojin ruwan kasar Koriya ta arewa suka tabbatar da kutsen da aka yi a tekun kasar, a kan hanyar komawa kasarsu, sojojin ruwa na kasar Koriya ta kudu sun fara yin harbi, a sakamakon haka, sojojin ruwa na Koriya ta arewa sun fara mayar da martani.

Hedkwatar kwamandan sojojin kasar Koriya ta arewa ta bayyana cewa, dole ne sojojin kasar Koriya ta kudu su nemi gafara daga kasar Koriya ta arewa, kuma ta dauki alhakin aikata wannan laifi.(Bako)