A ran 9 ga wata da dare a fadarsa, shugaban Amurka Barack Obama ya yi wani taron sirri da firaministan Isra'illa dake ziyara a kasar, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi kan yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya da batun nukiliya na Iran da sauransu.
Ofishin yada labarai na fadar shugaban Amurkar ya ba da sanarwar cewa, shugabannin biyu sun yi shawarwari kan batutuwa da dama dake shafar dangantaka tsakanin Amurka da Isra'illa. Barack Obama ya nanata alkawarin da ya yiwa Isra'illa a fannin tsaro, kuma ya yi shawarwari da Benjamin Netaniyahu a kan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu cikin lumana. Dadin dadawa, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya da batun nukiliya na Iran.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, kakakin Benjamin Netanyahu ya ki yin sharhi kan shawarwarin, kuma an soke taron manema labaru da Netanyahu zai yi a ran 10 ga wata.(Fatima)
|