Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 10:07:12    
Kasar Sin ta shaida wa duniya cewar ana iya tinkarar matsalar rashin abinci bisa kokari da mutane na wata zuriya suka yi

cri
A ran 9 ga wata, ofishin kasar Sin na hukumar tsara shirin samar da abinci ta M.D.D ya bayyana cewa, a ran nan, darekta mai gudanarwa ta hukumar Josette Sheeran ta bayar da wata sanarwa game da taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Josette Sheeran ta bayyana cewa, a dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka, an bayyana cewa jarin da aka zuba a fannonin samun ingancin abinci da aikin gona da manyan ayyukan yau da kullum zai taka muhimiyar rawa wajen warware matsalar rashin abinci a kasashen Afirka. A cikin sanarwar, an ce, kasar Sin ta samu sakamako a fannonin kyautata halin rashin isasshen abinci mai gina jiki da kara ingancin abinci, wannan ya shaida wa duniya cewar an iya tinkarar matsalar rashin abinci bisa kokari da mutane na wata zuriya suka yi.

A cikin sanarwar, an ce, hukumar tsara shirin samar da abinci ta M.D.D tana yi la'akarin kwafi wannan tsari, don ba da taimako ga manoma na yankuna da ke kudancin hamadar Sahara.(Abubakar)