Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 09:50:06    
Kwamitin sulhu na M.D.D. ya kalubalanci kungiyoyi daban daban da su aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya ta dukkan fannoni

cri
A ran 9 ga wata, kwamitin sulhu na M.D.D. ya kalubalanci kungiyoyi daban daban da su aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya ta dukkan fannoni wadda aka kulla a watan Maris na bana.

A ran nan, kwamitin sulhun ya yi taron a fili dangane da halin da ake ciki a yankin babban tafki na Afrika. A yayin taron, an saurari rahoton da manzon musamman na babban sakataren M.D.D. Ban Ki-moon kan batun yankin babban tafki na Afrika kuma tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya mika.

Mista Obasanjo ya bayyana cewa, sakamakon kokarin aiki da bangarori daban daban suka yi, a halin yanzu rikicin da ya bullo a yankin babban tafki a shekarar da ta gabata ya dan sassauta, kuma an kawar da damuwar yiwuwar abkuwar yaki. Amma halin da ake ciki a yankin ba ya da kyau, kuma ba a kawar da tushen rikicin ba. Idan ba a iya warware wadannan batutuwa da kyau ba, da wuya a iya tabbatar da zaman lafiya a cikin dogon lokaci.(Asabe)