A ran 9 ga wata, yayin da yake magana da 'yan jaridu, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi dake halartar taron ministoci a karo na hudu na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ya yi nuni da cewa, dandalin ya riga ya zama babban jigon yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su kyautata a wannan fanni a nan gaba.
Mista Yang ya bayyana cewa, dandalin hadin gwiwar wani muhimmin dandali ne dake jagorancin yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kana lamari ne dake sa kaimi ga samun hadin gwiwa tsakaninsu.
Dadin dadawa, minsta Yang ya nuna cewa, harkokin waje na Sin suna da ma'anar kiyaye samun babbar moriyar jama'ar Sin da ta kasa da kasa baki daya. Hakan ya sa ayyukan harkokin waje na Sin za su ci gaba da sa kaimi ga harkokin dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ba tare da fasawa ba, a yunkurin tabbatar da manufar taron ministoci a wannan karo tare da hukumomin da abin ya shafa.(Fatima)
|