Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 16:24:38    
Majalisar dokoki ta kasar Iraqi ta zartas da dokar zabe

cri
A ran 8 ga wata, majalisar dokoki ta kasar Iraqi ta zartas da dokar zabe da aka jinkirtar da ita sau da dama. Hakan ya kawar da cikas ga zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Janairu na shekara mai zuwa.

A cikin 'yan majalisar guda 195 da suka kada kuri'a, guda 141 sun kada kuri'ar amincewa, sannan aka zartas da dokar zabe wadda ake rikici a kanta. Da akwai kujeru 275 a majalisar dokoki ta Iraqi.

Bisa dokar zabe da aka zartas a ran 8 ga wata, za a gudanar da zabe a farkon shekara mai zuwa a yankin Kirkouk bisa sunayen masu kada kuri'a da aka yi wa rajista a shekarar 2009. A sa'I daya kuma, dokar zabe ta tabbatar da cewa za a gudanar da zaben ta hanyar bayyana sunayen 'yan takara a fili, wato za a bayyana sunayen 'yan takara da jam'iyyunsu a fili.

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya yi marhabin da zartas da dokar, kuma yana ganin cewa, hakan zai ba da taimako ga rundunar tsaro ta Iraqi da ta karbi ayyukan tsaro, kuma yawancin sojojin Amirka za su janye jiki daga kasar bayan zaben.

A ran 8 ga wata, ta hannun kakakinsa, babban sakataren M.D.D. Ban Ki-moon ya bayar da sanarwar yin maraba da zartas da dokar zaben, kuma ya yi kira ga jam'iyyun siyasa daban daban na Iraqi da su yi kokarin shiga zaben da za a gudanar a farkon shekara mai zuwa.(Asabe)