A ran 8 ga wata, shugaban Algeriya Abdelaziz Bouteflika ya bayyana cewa, kasar Algeriya ta nuna babban yabo ga kasar Sin da ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka domin samun adalci a cikin harkokin duniya, musamman ma a cikin shawarwari na Doha.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na gwamnatin Algeriya ya bayar, an ce, a gun bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka yi a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar, ministan tsaron kasar Algeriya, kana wakilin shugaban kasar Abdul-Aziz Belkhadem ya karanta bayanin malam Abdel Aziz Bouteflika, inda ya yi kira ga kasashen Afirka da Sin da su kara mu'amala a fannin tarbiyya da ma'aikata da kafofin yada labaru da hukumomin nazari, a yunkurin kara samun fahimta da girmama juna.(Fatima)
|