Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 10:19:34    
Shugaban kwamitin tarayyar Afrika ya nuna yabo ga kokarin da Sin ta yi wajen tabbatar da alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika

cri
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, an yi taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa kan hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika daga ran 8 zuwa 9 ga wata a birnin Sharm El Sheikh dake mashigin teku na kasar Massar, kungiyar tarayyar Afrika da kasashen Afrika daban-daban sun nuna babban yabo ga kokarin da Sin ta yi wajen cika alkawarin da ta yi, da kuma taimakon da ta baiwa kasashen Afrika domin neman samun bunkasuwa.

A ran 8 ga wata a Sharm El Sheikh na kasar Massar, a gun taron da aka yi a wannan rana, shugaban kwamitin tarayyar Afrika Jeam Ping ya furta cewa, kasar Sin ta kan dukufa kan cika alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika, kwamitin ya nuna matukar girmamawa ga kokarin da gwmanatin Sin ta yi wajen tabbatar da shirin Beijing na dandalin daga shekarar 2007 zuwa 2009 a duk fannoni.

Shugaban kasar Sudan ya yi jawabi cewa, a 'yan shekarun nan, gwamantin Sin ta taka rawa wajen kara kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika da kuma ba da taimako ga ayyukan bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika. Dadin dadawa, kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi a dandalin wajen taimakawa kasashen Afrika.

Ban da wannan kuma, shugaban hukumar zuba jari da harkokin yankin ba tare da biyan haraji ba Mr Osama Saleh ya shedawa manema labaru cewa, Massar tana ci gaba da bunakasa dangantakar sada zumanci dake tsakaninta da Sin, kuma ta mayar da Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da suka fi zuba jari a kasar, saboda haka, Massar ta nuna maraba ga dukkan kamfanoni da za su zuba jari a kasar.

A kwanakin baya, gwamnan jihar Harare na kasar Zimbabwe David Karimanzira ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan sabbin matakan da aka gabatar a wajen taron za su inganta hadin gwiwa tsakanin Zimbabwe da Sin zuwa wani sabon matsayi.(Amina)