A ran 8 ga wata, gwamnatin Congo(Kinshasa) ta bayar da sanarwar cewa, a ran 6 ga wata, a birnin Kinshasa, gwamnatin kasar da kungiyar MONUC sun kafa asusun farfadowa da kwanciyar hankali, don ba da taimako ga tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a yankin gabashin kasar.
A cikin sanarwa, an ce, a ran 6 ga wata, firayim ministan kasar Congo(Kinshasa) Adolphe Muzito da wakilin musamman mai kula da harkokin Kongo Kinshasa na babban sakataren MDD Alan Doss sun halarci bikin kafa asusun, kuma sun sanar da kafa kwamitin kula da harkokin asusun.
A madadin gwamnatin kasar Congo(Kinshasa) Adolphe Muzito ya nuna godiya ga M.D.D da kasashen duniya. Ya ce, sabo da kafuwar asusun farfadowa da kwanciyar hankali, kasar Congo(Kinshasa) za ta tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa cikin sauri, ta yadda jama'ar kasar za su kara cin moriya.(Abubakar)
|