Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 09:54:24    
Shugaban kasar Masar ya gabatar da ka'idoji 10 na yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin

cri
A ran 8 ga wata, shugaban kasar Masar Mohammed Hosni Mubarak ya yi wani jawabi, yayin bikin kaddamar da taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a karo na 4, inda ya gabatar da ka'idoji 10 don inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin da samun bunkasuwa mai dorewa.

Ka'idojin sun hada da ta girmama juna da hadin gwiwa da samun moriyar juna, da ci gaba da yin shawarwari kan hadin gwiwarsu, da kokarin cimma daidaito kan ra'ayoyinsu, da kiyaye moriyar jama'ar Afirka da ta Sin, kuma sai batun kasashen Afirka da kasar Sin su yi kokari tare wajen zurfafa ra'ayin demokuradiyya kan huldar dake tsakanin kasa da kasa, sannan su nuna amincewa ga bangarori biyu a fannonin siyasa da tattalin arziki da dai sauransu.

Ka'idojin 10 sun bukaci kasashen Afirka da kasashe masu tasowa su samu ikon shiga kungiyoyin tattalin ariziki da hada-hadar kudi na duniya musamman kungiyar kasashe 8 da kungiyar G20. Kuma a kawo karshen matakan ba da kariya ga cinikayya da kasashe masu ci gaba suke dauka, musamman matakai game da kayayyaki da amfanin gona da suke fitarwa zuwa ga kasashen Afirka. Kana a tsaya tsayin daka kan matakin sa kasashen Afirka su samu fasahohi da gudummawar kudi da suke bukata don tinkarar sauye-sauyen yanayi.(Zainab)