Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 09:46:20    
Kungiyar Tehrik-e-Taliban ta Pakistan ta dauki alhakin aiwatar da harin kunar bakin wake a Peshawar

cri
A ran 8 ga wata, kungiyar Tehrik-e-Taliban ta Pakistan ta sanar da dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a Peshawar babban birnin jihar Brazial dake iyakar kasa dake arewa maso yammancin kasar.

Kakakin kungiyar ya shedawa manema labaru na wurin ta wayar tarho cewa, sakamakon kafa kungiyar sojojin sa kai da shugaban garin Adizai dake karkarar birnin Peshawar Abdul Malik ya yi wadanda ke nuna goyon bayan matakan sojoji kan kungiyar da gwamnatin Pakistan ta dauka, hakan ya sa birnin Peshawar ya zama wajen da aka kai masa hari.

Bisa kididdigar da sojan kasar Pakistan suka bayar, an ce, wannan hari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, yayin da wasu 15 suka ji rauni. Sojoji sun fadi cewa, wanda ya kai hari ya ta da bom ne kusa da motar Abdul Malik, lamarin da ya sa Malik din ya ji rauni sosai, amma bayan da aka kai shi asibiti ya mutu saboda matsanancin halin da ya kasance a ciki.Shugaban kasar Pakistan Mr Asif Ali Zardali da firayim ministan kasar Yusuf Raza Gillani sun sanar da yin Allah wadai da abkuwar lamarin.(Amina)