Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 08:59:15    
Shugaban kwamitin tarayyar Afrika ya nuna yabo ga kokarin da Sin ta yi domin tabbatar da alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika

cri
A ran 8 ga wata a Sharm El Sheikh na kasar Massar, a gun taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa kan hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika da aka yi a wannan rana, shugaban kwamitin tarayyar Afrika Jean Ping ya furta cewa, kasar Sin ta dukufa kan cika alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika, kwamitin ya nuna girmamawa ga kokarin da gwmanatin Sin ta yi wajen tabbatar da shirin Beijing na dandalin daga shekarar 2007 zuwa 2009 a duk fannoni.

Ban da wannan kuma, Jean Ping ya fadi cewa, kasar Sin ta kan nuna goyon baya ga samun bunkasuwar kasashen Afrika, kuma a sakamakon dukufarta kan cika alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika, kasar Sin ta tabbatar da shirin Beijing a duk fannoni.

Dadin dadawa, Jean Ping ya nuna yabo ga goyon baya da Sin ta nuna wa kwamtin.(Amina)