A kwanakin baya, gwamnan jihar Harare ta kasar Zimbabwe David Karimanzira ya bayyanawa 'yan jaridar kasar Sin cewa, kasarsa tana fatan sabbin matakan da aka gabatar a wajen taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a karo na 4 a birnin Alkahira za su inganta hadin gwiwa tsakanin Zimbabwe da Sin zuwa wani sabon matsayi.
A ran 6 ga wata, Karimanzira ya kai ziyara wajen bikin nunin hotuna kan nasarorin da aka samu bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a ofishin jakadancin Sin dake a kasar Zimbabwe. Ya kuma bayyana cewa, an sheda daga hotunan cewa, a karkashin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Zimbabwe da Sin an samu ci gaba a shekaru 3 da suka wuce. Ya yi imani cewa, sabbin matakan da aka gabatar a taron ministoci za su inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, wanda zai inganta tattalin arzikin Zimbabwe.(Zainab)
|