Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 21:11:31    
Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Sudan a fannin man fetur ya kawo moriyar juna, a cewar Wen Jiabao

cri

A ran 7 ga wata da dare a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da shugaban kasar Sudan Omar Hassan Ahmed Al-Bashir, inda ya ce, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Sudan a fannin man fetur ya kawo moriyar juna.

Wen Jiabao ya ce, kasashen Sin da Sudan suna da huldar abokantaka ta gargajiya, ya kamata kasashen biyu su habaka hadin gwiwarsu don ingiza bunkasuwar huldarsu. Kasar Sin tana son taka rawa mai yakini kan aikin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman samun bunkasuwa a kasar Sudan.

Omar Hassan Ahmed Al-Bashir ya ce, zuba jari da kasar Sin ta yi a kasar Sudan ya kawo moriya ga jama'ar kasar, wanda kuma ya samu maraba sosai daga wajensu. Kasar Sudan tana fatan za ta kara yin hadin gwiwa tare da Sin a fannonin makamashi da aikin gona da manyan ayyukan yau da kullum da dai sauransu. Haka kuma, kasar Sudan ta nuna babban yabo ga matsayin da Sin ta dauka kan batun Darfur da kuma tallafin da kasar Sin ta samar mata, kasar Sudan za ta ci gaba da ingiza batun Darfur a fannin siyasa da yunkurin shimfida zaman lafiya a tsakanin yankunan arewa da kudu na kasar.(Lami)