Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 20:59:46    
Ya kamata gamayyar kasa da kasa su tabbatar da hali mai kyau ga kasar Zimbabwe don shimfida zaman lafiya a kasar, a cewar Wen Jiabao

cri

A ran 7 ga wata da dare a birnin Sharm El-Sheikh, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe, inda ya ce, kasar Sin tana fatan kasar Zimbabwe za ta iya samun ci gaban yunkurin shimfida zaman lafiya a gida don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwa.

Wen Jiabao ya kara da cewa, a matsayin wata kawar kasar Zimbabwe, kasar Sin ta samar da tallafi don kyautata zaman rayuwar jama'ar Zimbabwe da ingiza farfadowar kasar da kuma sake raya ta. Kasar Sin za ta ci gaba da kara yin hadin gwiwa da kasar Zimbabwe don ciyar da huldar a tsakanin kasashen biyu gaba.

Robert Gabriel Mugabe ya bayyana cewa, jama'ar kasar Zimbabwe sun nuna godiya ga tallafin da kasar Sin ta samar, kuma sun darajanta zumuncin dake kasancewa a tsakanin kasashen biyu. Kasar Zimbabwe tana son ci gaba da tuntubar kasar Sin don kara yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ciniki da zuba jari da aikin gona da kuma sana'ar kire-kire da dai sauransu.(Lami)