|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-11-08 20:55:12
|
Sin tana fahimtar matsayi da kuma bukatun kasashen Afirka a kan batun sauyewar yanayi
cri
Yayin da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ke ganawa da takwaransa na kasar Habasha Meles Zenawi a ran 8 ga wata da safe bisa agogon wurin a birnin Sharm El Shaikh na kasar Masar, ya bayyana cewa, kasar Sin tana fahimta da kuma goyon bayan matsayi da bukatun kasashen Afirka a kan batun sauyewar yanayi, kuma tana son inganta hadin gwiwa tare da Afirka domin sa kaimi ga samun ci gaba a yayin taron Copenhagen bisa ka'idar daukar nauyi tare amma akwai bambanci.
A nasa bangaren kuma Mr. Meles ya furta cewa, kasar Habasha tana son inganta tuntuba da hadin gwiwa tare da kasar Sin a kan batun sauyewar yanayi.(Kande Gao)
|
|
|