Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 20:40:32    
Kasar Sin tana son bayar da gudummawa wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya mai dorewa a kasar Congo Kinshasa

cri
Yayin da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ke ganawa da takwaransa na kasar Congo Kinshasa Adolphe Muzito a ran 7 ga wata da dare bisa agogon wurin a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, ya bayyana cewa, kasar Sin na son bayar da gudummawar da ta dace wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya mai dorewa a kasar Congo Kinshasa.

Wen Jiabao ya ce, kasashen Sin da Congo Kinshasa suna iya ba da taimako ga juna a fannin tattalin arziki, kuma akwai kyakkyawar makoma wajen hadin kansu don moriyar juna. Ana yin imanin cewa, bisa kokarin da kasashen biyu ke yi, dangantakar da ke tsakaninsu za ta kara samun kyautatuwa.

A nasa bangaren kuma Mr. Muzito ya furta cewa, kasar Congo Kinshasa na fatan kiyaye yin cudaya a tsakanin manyan jami'ai na kasashen biyu, da kuma inganta hadin kansu bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Kasar Congo Kinshasa tana maraba da masana'antun Sin da su zuba jari a kasar, da kuma sa hannu a cikin ayyukan raya kasar a fannonin ayyukan gona da samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa da raya muhimman ayyukan yau da kullum kana da raya albarkatun ma'adinai.(Kande Gao)