Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 17:08:02    
Firayim ministocin Sin da Masar sun halarci babban taron 'yan masana'antu na Sin da Afirka

cri
A ran 7 ga wata bisa agogon wurin, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao da takwaransa na kasar Masar Ahmed Nazef sun halarci bikin bude babban taro a karo na uku na 'yan masana'antun Sin da Afirka a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, inda Wen Jiabao ya yi jawabi mai lakabi "inganta hadin gwiwa don moriyar juna, da kuma sa kaimi ga samun bunkasuwa don samun nasara tare".

Wen Jiabao ya bayyana cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata, kasar Sin ta kebe rabin kudin da ta bai wa Afirka a fannin ayyukan jin dadin jama'a. Cibiyoyin gwaji goma a fannin ayyukan gona da kasar Sin ta kafa sun sa jama'ar Afirka su ga fatan alheri na fitowa daga mawuyacin hali na jin yunwa, makarantu 100 da Sin ta kafa a yankunan karkara sun sa yara dubu 30 na Afirka su samu damar karatu, haka kuma cibiyoyi 30 na shawo kan cutar malariya sun kawo alheri ga jama'a fiye da miliyan dari na Afirka.

Haka kuma Wen Jiabao ya ce, Sin za ta kara kyautata aikin tallafawa Afirka, da kuma kara dora muhimmanci kan hada aikin hadin gwiwa tare da Afirka kan tattalin arziki da cinikayya da musanyar fasahohi tare domin kyautata kwarewar Afirka a fannin raya kansu.

A gun bikin taron kuma, firayim ministan kasar Masar Ahmed Nazef ya bayyana cewa, ana fatan Sin da Afirka za su iya kara yin mu'amala a tsakaninsu. Kuma ana maraba da Sin da ta gudanar da dimbin ayyuka a Afirka.(Kande Gao)