A ran 7 ga wata a birnin Moscow, a yayin da shugaban kasar Rasha Dimitrij Medvedev yake ganawa da manema labaru, ya ce, idan kasar Iran ba ta dauki matakan da suka dace da batun naukiliya ba, ba za a yi watsi da shirin sanya mata takunkumi ba.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na ITAR-TASS ya bayar, an ce, Dimitrij Medvedev ya ce, idan ba za a samu sakamako a kan batun nukiliya na kasar Iran ba, akwai yiwuwar kakabawa kasar Iran takunkumi. Amma ya jaddada cewa, kasar Rasha ba ta fatan za a daidaita batun ta hanyar sanya wa Iran takunkumi ba, sabo da hakan zai kara tsanantar batun.(Lami)
|