Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 16:55:02    
Shugaban kasar Mauritius ya gana da Mr. Wang Zhaoguo

cri

Ran 7 ga wata a Port Louis, babban birnin kasar Mauritius, shugaba Anerood Jugnauth na kasar ya gana da Mr. Wang Zhaoguo memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma mataimakin shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Mauritius.

Mr. Wang Zhaoguo ya ce, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Mauritius domin kara yin musayar manyan jami'ai, da fadada hadin gwiwa kan fannoni daban daban, da ci gaba da daidaita matsayinsu kan manyan harkokin duniya, da moriyar jama'ar kasashen biyu. Game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ya ce, kasar Sin tana son hada kanta tare da kasashen Afirka domin ci gaba da ba da gudummawa wajen cimma nasarar taron ministoci a karo na 4 na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, tare da sa kaimi ga bunkasuwar sabuwar huldar amincewa da ke tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare.

Mr. Jugnauth ya nuna godiya ga taimako da goyon bayan da kasar Sin ta bayar ga kasar Mauritius, kuma ya gaskata cewa huldar da ke tsakanin kasashen biyu za su sami ci gaba, ban da haka kuma, kasar Mauritius tana son ci gaba da karfafa musayar da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Ban da haka kuma, Mr. Wang Zhaoguo ya yi shawarwari tare da Mr. Purryag shugaban majalisar dokoki ta kasar Mauritius a wannan rana. [Musa Guo]