Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-07 18:30:24    
Kungiyoyin siyasa daban-daban a Madagascar sun cimma yarjejeniyar karshe kan raba madafun iko

cri
Da sanyin safiyar ranar 7 ga wata, a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, shugabannin manyan kungiyoyin siyasa hudu a kasar Madagascar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar raba madafun iko a hukunce, lamarin da ya taimaka sosai wajen kawo karshen rikicin siyasar da ya shafe watanni da dama yana addabar kasar.

Bisa wannan yarjejeniya, jagoran gwamnatin Madagascar na yanzu Andry Rajoelina zai ci gaba da zama shugaban hukumar iko ta rikon-kwarya ta kasar, amma mutane daga kungiyoyin tsoffin shugabannin kasar Marc Ravalomanana, da Albert Zafy za su zama shugaban hadin-gwiwa na farko da shugaban hadin-gwiwa na biyu, haka kuma magoyin bayan tsohon shugaban kasar Didier Ratsiraka, wato Eugene Mangalaza zai jagoranci wata gwamnatin gamin-gambiza wadda ke kunshe da ministoci 31. Har wa yau kuma, nan ba da dadewa ba za'a kafa majalisar dokokin rikon-kwaryar kasar wadda ke kunshe da membobi 258.

A wannan rana kuma, wakilin musamman daga kungiyar raya kudancin Afirka SADC wanda ke kula da harkokin daidaita rikicin siyasar Madagasacar, kana tsohon shugaban kasar Mozambique Joachim Chissano ya bayyana cewa, cimma yarjejeniyar raba madafun iko tsakanin kungiyoyi daban-daban a Madagascar zai taimaka sosai wajen samar da kyakkyawar makoma ga kasar.(Murtala)