Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-07 17:26:29    
An kaddamar da bukin nunin hotuna kan nasarorin da aka samu ta fannin aiwatar da matakai biyo bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka a Abuja

cri
Ranar 6 ga wata, a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya, ofishin jakadancin Sin dake kasar ya kaddamar da bukin nunin hotuna na tsawon mako guda kan nasarorin da aka samu ta fannin aiwatar da matakai biyo bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka.

A wajen kaddamar da bukin nunin hotunan, jakadan Sin dake Nijeriya Mista Xu Jianguo ya yi jawabin cewa, bayan da aka gudanar da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka, ana ci gaba da daukar matakai daga fannoni daban-daban domin karfafa hadin-gwiwar bangarorin biyu, haka kuma ana aiwatar da muhimman manufofi 8 da gwamnatin Sin ta dauka domin inganta hadin-gwiwa a tsakaninta da kasashen Afirka yadda ya kamata. Ayyukan cude-ni-in-cude-ka da ake yi tsakanin Sin da Nijeriya sun kunshi yankin cinikayya maras shinge, da asibitoci, da manyan ayyukan gona, da makarantun firamare a kauyuka, da cibiyoyin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da sauransu, wadanda za su kawo babbar moriya ga jama'ar kasar Nijeriya.(Murtala)