Jami'in musamman mai ba da taimako ga shugaban Barack Obama na kasar Amurka wato Jeffrey Bader ya yi wani jawabi a ran 6 ga wata cewa, sai da kasar Korea ta arewa ta yarda da yin shawarwari da Amurka bisa makasudin watsi da shirin kera makaman nukiliya ne kawai, kasar Amurka za ta yi shawarwari irin na bangarori biyu da Korea ta arewa.
Bader ya yi wannan bayani ne a hukumar Brookings, inda ya ce, kasar Amurka ba ta da sha'awar yin shawarwari da kasar Korea ta arewa ba bisa makasudin watsi da shirin kera nukiliya ba. Ya ce, manzon musamman na kasar Amurka kan matsalar nukiliya ta Korea ta arewa Mr. Stephen Bosworth yana shirin ganawa da jami'an Korea ta arewa bisa tsarin yin shawarwari a tsakanin bangarori shida kan matsalar nukiliya ta Korea ta arewa, amma yanzu ba a tabbatar da lokaci da kuma hanyar da za a bi domin yin shawarwarin ba tukuna.(Danladi)
|