An shirya taron manyan jami'ai a karo na 7 na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka a birnin Sharm el-sheik na kasar Masar a ran 6 ga wata, an shirya wannan taro ne domin share fage ga taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, wanda za a shirya bayan kwanaki biyu.
Wannan taron manyan jami'ai ya zartas da shirin ajandar taron ministoci. Ban da wannan kuma an zartas da shirin rahotannin 'sanarwar Sharm el-sheik', da 'shirin daukar matakai daga shekarar 2010 zuwa 2012 na Sharm el-sheik', wadanda za a gabatar da su a gun taron ministoci da za a shirya domin dudduba su, haka kuma za a sanar da su a gun taron ministoci. Kasar Sin ta gabatar da rahoto kan aikin gaba dangane da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka.(Danladi)
|