Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-07 17:12:48    
An kaddamar da bukin baje-koli kan harkokin cinikayya na kasa da kasa na shekara ta 2009 a birnin Lagos na kasar Nijeriya

cri
Ranar 6 ga wata, a cibiyar nune-nune kan harkokin cinikayya na kasa da kasa dake birnin Lagos na tarayyar Nijeriya, an kaddamar da bukin baje-koli kan harkokin cinikayya na kasa da kasa na shekara ta 2009.

Babban taken bukin a wannan shekara shi ne, "yin amfani da sabon zarafi domin tinkarar rikicin kudi na duniya". Bukin dai na tsawon yini 10 zai samu halartar masana'antu sama da 100 daga kasashe fiye da 10, wadanda ke kunshe da kasashen Sin, da Thailand, da Pakistan, da Kenya, da Afirka ta Kudu, da Cote D'ivoire, da Senegal, da Ghana da sauransu, ciki kuwa har da masana'antun Sin kusan 100. Har ila yau kuma, akwai masana'antun kasar Nijeriya sama da 300 wadanda za su halarci bukin.

An yi hasashen cewa, akwai 'yan kallo fiye da miliyan 1.5 wadanda zasu kai ziyara bukin baje-koli a wannan gami. Haka kuma, bukin baje-koli na kasa da kasa da za'a yi a wannan karo zai kasance bukin da ya fi samun halartar masana'antun Sin tun da aka fara yinsa.(Murtala)