Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-07 17:11:36    
Ra'ayoyin MDD kan Afghanisatan da zirin Gaza da za a gabatar a ran 6 ga wata

cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana a ran 6 ga wata a birnin New York, hedkwatar MDD cewa, ko da yake halin da ake ciki a kasar Afghanistan ya kara lalacewa, amma MDD ba za ta janye ma'aikata daga kasar ba, amma MDD tana daukar matakai cikin gaggawa domin tabbatar da zaman lafiyar ma'aikatarta da ke aiki a Afghanistan.

Ban Ki-moon ya yi wannan bayani ne bayan da ya halarci taron yin shawarwari cikin sirri kan batutuwan Afghanistan na kwamitin sulhu na MDD. A daidai wannan lokaci, Mr. Ban Ki-moon ya gaya wa manema labaru cewa, bisa bukatar babban taro na MDD, zai gabatar da rahoto da kungiyar bincike kan rikici a zirin Gaza ta MDD ta yi ga kwamitin sulhu cikin sauri, amma bai sanar da cikakken bayani ba. A ran 5 ga wata, babban taro a karo na 64 na MDD ya zartas da wani kuduri, inda aka bukaci Isra'ila da Palesdinu da su dauki matakai a cikin watanni 3 masu zuwa domin bincike kan lamuran da suka saba wa hakkin 'dan Adam da dokokin duniya a yankunansu, haka kuma an bukaci Ban Ki-moon gabatar da rahoto da kungiyar bincike kan rikici a zirin Gaza ta MDD ta yi ga kwamitin sulhu.

A ran 6 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya bayar da wata sanarwa, inda aka sa kaimi ga sabuwar gwamnatin kasar Afghanistan da ta dauki matakai masu amfani domin tinkarar babban kalubale a gaban kasar.

Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu na MDD ya sanya ran hada kai da shugaba Hamid Karzai na kasar da kuma sabuwar gwamnatinsa, kwamitin sulhu ya jaddada cewa, tilas ne sabuwar gwamnatin kasar Afghanistan ta sake kaddamar da yunkurin siyasa bisa tsarin mulkin kasa da tabbatar da shigar jam'iyyu daban daban, domin samar da hadin kai da zaman lafiya da albarka a kasar.(Danladi)