Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 21:25:07    
An yi bikin gabatar da hotunan da suka bayyana ci gaban da aka samu a aikin gaba dangane da taron koli na Beijing na dandalin hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika a birnin Nairobi

cri

A ran 6 ga wata a birnin Nairobi, ofishin jakadancin Sin dake kasar Kenya ya yi bikin gabatar da hotunan da suka bayyana ci gaban da aka samu a aikin gaba dangane da taron koli na Beijing na dandalin hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika. Jami'an gwamnatin kasar Kenya, da jakadun kasashen Afirka da ke a kasar Kenya, da kwararru a wurin da dai sauransu sun halarci bikin.

Jakadan kasar Sin da ke Kenya Mr. Deng Hongbo ya ce, gwamnatin kasar Sin ta sanar da matakai 8 da za ta dauka na karfafa hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, wadannan matakai sun shafi cinikayya da zuba jari da yin mu'amalar kwararru da dai sauran fannoni. Kasar Sin ta ba da kudin taimako da na rance na alfarma don gudanar da manyan ayyuka da kiwon lafiya a kasar Kenya, wadanda suka biya bukatar jama'ar kasar Kenya, tare da samar da alheri gare su.(Danladi)