|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-11-06 16:06:34
|
Allurar rigakafin cutar murar A(H1N1) ba ta da hadari ko kadan
cri
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, a ran 5 ga wata, jami'in hukumar lafiya ta duniya Keiji Fukuda ya furta a Geneva cewa, allurar rigakafin cutar murar A(H1N1) ba ta da hadari ko kadan, kuma tana da amfani sosai.
Keiji Fukuda, yanzu shi ne mai ba da taimako na musamman na babbar jami'ar hukumar Margaret Chan kan harkokin cutar. Ya shedawa manema labaru a wannan rana cewa, kawo yanzu dai, an riga an yi allurar ga mutane fiye da miliyan daya na kasashe 20 ko fiye, babu wani mutumin da ya kumu da rashin lafiya, an fahimci cewa wannan allura ba ta da hadari ko kadan.
Dadin dadawa, ya fadi cewa, ga dukkan alamu, a yanzu, cutar murar A(H1N1) ta zama cuta da ta fi tsananta a duniya.(Amina)
|
|
|