An samu abkuwar harbe-harbe a wani sansanin sojojin kasa na Fort Hood dake jihar Texas ta kasar Amurka a ran 5 ga wata, bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar suka bayar, an ce, lamarin ya haddasa mutuwar mutane 12, kuma mutane 31 sun ji rauni. Lamarin ya tayar da hankalin shugaban kasar Barack Obama, inda ya ce, wannan lamari ya girgiza dukkan jama'a.
Shugaban sansanin Bob Cone ya bayyana a wajen taron manema labaru da aka yi a wannan rana cewar, da karfe daya da rabi na yamma a cibiyar horar da sojojin sansanin, wani soja dake dauke da bindigogi biyu ya yi harbin kan mai uwa da wabi, a lokacin da wasu sojojin da suka kammala karatun jami'a a wani dakin cibiyar ke gudanar da bikin kammala karatu. Mr Cone ya ce, an harbe wanda ya yi harbin har lahira, kuma an kama mutane biyu da suke aikata laifin. Har yanzu dai, ba a san wanda ya yi harbin sosai ba, Cone ya bayyana cewa, tilas ne a yi bincike game da lamarin.(Zainab)
|