Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 09:30:45    
Firayim ministan kasar Zimbabwe ya sanar da yin watsi da nuna adawa da gwamantin hadin kai

cri

A ran 5 ga wata a Maputo babban birnin kasar Mozambique, firayim ministan kasar Zimbabwe Morgan Richard Tsvangirai ya sanar da cewa, jam'iyyar MDC dake karkashin jagorancinsa ta yi watsi da nuna adawa da gwamnatin hadin kai.

Morgan Richard Tsvangirai ya yi wannan furuci ne a ran 4 ga wata, a gun taron manema labaru da aka yi bayan da ya halarci taron shugabanni da kungiyar SADC ta yi domin daidaita korafe-korafe dake kasancewa a cikin gwamnatin hadin kan kasar Zimbabwe a kwanan baya. Inda ya sanar da cewa, kungiyar SADC ta yanke shawarar jam'iyyu 3 mafi girma a kasar Zimbabwe za su yi taro a cikin kwanaki 15 masu zuwa domin tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar sulhuntawa ta fuskar siyasa a duk fannoni, kuma za su shawo kan dukkan matsaloli cikin kwanaki 30.

Dadin dadawa, a ran 5 ga wata, kungiyar ta yi imani da cewa, kawo yanzu dai, ko da yake gwamnatin hadin kai ta Zimbabwe tana fuskantar batutuwa da dama, amma tana iya shawo kan dukkan batutuwa da kanta.(Amina)